Ya kamata Nijeriya ta kwaikwayi kasar Koriya ta Kudu inda shugaban kasa ya ke shekaru 5 kacal ya sauka a zaɓi wani – Peter Obi
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sake jaddada bukatar kafa tsarin wa’adin shekara 5 kacal ga shugaban ƙasa a Najeriya.
Obi ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Bauchi lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi.
Ya ce kamata ya yi a soke tsarin wa’adi biyu, maimakon shekara 4 ya zama shekara 5 kai tsaye, kamar yadda ake yi a ƙasar Koriya ta Kudu.
Obi, wanda ke da niyyar sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027, ya ce idan ya samu nasara ba zai yi fiye da wa’adin da aka kayyade masa ba, yana mai jaddada cewa ba zai ƙara ko kwana guda sama da shekara 4 ba a ofis.
Comment:realy it is good for us.