Wasu ’yan bindiga dauke da makamai sun kai wa direban tirela, Dallami Yunusa, hari a Ogi Junction, karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo, inda suka ji masa rauni sannan suka banka wa motarsa wuta.
Shugaban sashen jigilar manyan motoci na NURTW a Okigwe, Dahiru Musa Raza, ya ce lamarin ya faru ne bayan motar direban ta samu matsala, inda ya tafi neman maigyara. A lokacin gyaran mota, wasu maharan biyu dauke da adduna suka iso kan babur, suka tarwatsa masu gyara, sannan suka kai wa direban hari.
Rahoton jaridar Daily Trust yace sojoji daga Okigwe sun isa wurin, inda suka tsinci direban da rai kuma suka garzaya da shi asibiti. Daga baya an kai shi Dala Orthopedic a Kano don samun kulawa.
An mika rahoton lamarin ga ’yan sanda, duk da cewa kakakin rundunar a Imo, Henry Okoye, ya ce bai samu cikakken bayani ba tukuna.



