Ma’aikatar Harkokin Addini ta Bangladesh ta mayar da Taka dubu 46,725 ga kowane mahajjacin bana, bayan rage kuɗin masauki a Saudiyya.
Jimillar kuɗin da aka mayar ta kai Taka miliyan 82, wanda ya yi daidai da sama da Naira dubu 500 ga kowane mahajjaci.
Mai ba da shawara kan harkokin addini, AFM Khalid Hossain, ya ce wannan nasarar ta biyo bayan bin dokokin Saudiyya da kuma biyan kuɗin Hajj akan lokaci.
A bana, mahajjata 87,100 daga Bangladesh ne suka halarci Hajj, inda kuɗin shirin ya ragu da Taka 73,000 ga kowane mutum idan aka kwatanta da bara.
Sun kuma samu masauki kusa da Ka’aba tare da sabbin hidimomi kamar manhajar Labbike, layin waya, da katin biyan kuɗi na Hajj.