Dakarun Operation Safe Haven a Jihar Plateau sun kama wani Musa Ali a Jos bisa zargin sojan gona da sunan jami’in su domin yin zamba.
Mai magana da yawun OPSH, Manjo Samson Zhakom, ya bayyana cewa Musa ya karɓi N400,000 daga dangin wani mai safarar makamai da ke tsare, inda ya yi musu ƙarya cewa zai iya dakatar da bincike da kuma sakin wanda ake tsare da shi.
Jsridar Daily Nigerian ta ce jami’an rundunar sun samu labarin irin aikin da mutumin yake, kafin daga bisani aka cafke shi, kuma za a gurfanar da shi kotu bayan kammala bincike.
Hukumar ta gargadi jama’a da su yi hattara da masu badda kama da sunan sojoji su na zambatar mutane.




