Rahotanni sun bayyana cewa rundunar sojin Mali ta kama akalla sojoji 20 da ake zargi da shirin kifar da gwamnatin mulkin soja ta Colonel Assimi Goita.
Wata majiya ta tsaro ta ce an fara kamen tun kusan kwanaki uku da suka gabata, inda aka samu wadanda ake zargi da yunkurin tada fitina a cikin gwamnati.
Daga cikin wadanda aka kama har da tsohon gwamnan lardin Mopti, Janar Abass Dembele, wanda aka dauke shi daga gidansa a Kati, kusa da Bamako, ba tare da bayyana masa dalilin kama shi ba.
Mali ta dade tana fama da rikice-rikicen tsaro tun 2012, ciki har da hare-haren ’yan bindiga masu ikirarin jihadi, rikicin kabilanci, da matsalar tattalin arziki kamar yadda rahoton gidan talabijin na Channels ya tattaro.



