Mai ba shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yada labarai, Daniel Bwala, ya bayyana cewa tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ba zai iya kayar da Tinubu a zaben 2027 ba.
Bwala, wanda tsohon mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ne a zaɓen 2023, ya yi wannan bayani ne a hirar da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels Laraban nan.
Ya gargadi Jonathan da kada ya saurari waɗanda ke ƙarfafa masa gwiwar tsayawa takara, yana mai cewa akwai wasu marasa gaskiya da ke ƙoƙarin jawo hankalin tsohon shugaban ƙasar Jonathan ya dawo domin tsayawa takara.
Bwala ya ce, ko da Jonathan bai bayyana niyyarsa ba, idan ya tsaya takara ba zai iya kayar da Tinubu ba.