Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya karɓi bakuncin Ngozi Okonjo-Iweala a Fadarsa dake Abuja a ranar Alhamis.
Tinubu da Okonjo-Iweala sun shiga tattauna kan batutuwan cinikayya masu muhimmanci ga ƙasa da nahiyar Afrika da ma duniya baki ɗaya.
Tattaunawar shugaba Tinubu da Okonjo-Iweala ya zo ne makonni biyu kafin karewar wa’adinta na farko a ranar 31 ga watan Agustan nan na 2025, kafin ta fara wa’adinta na biyu a ranar 1 ga Satumba, 2025.
Okonjo-Iweala ta kafa tarihi a shekarar 2021 a matsayin ‘yar Afirka ta farko kuma mace ta farko da ta shugabanci Kungiyar ta kasuwanci ta Duniya WTO.