Hukumomin tsaron kasar Mali sun ce sun kama manyan hafsoshin soji biyu, sojoji masu yawa da wasu fararen hula, ciki har da wani da ake zargin ɗan leken asirin Faransa ne, bisa zargin shirin tada rikici a ƙasar. Ministan tsaron kasar Janar Daoud Aly Mohammedine ya bayyana a talabijin na ƙasar cewa waɗannan mutane sun samu taimako daga wasu ƙasashen waje, inda ya bayyana sunan ɗan ƙasar Faransa Yann Christian Bernard Vezilier a matsayin wanda yake aiki wa hukumar leken asirin Faransa. Hukumomin na Mali sun ce an fara wannan shiri tun ranar 1 ga watan Agusta, kuma yanzu an kawo ƙarshensa gaba ɗaya, tare da nuna hotunan waɗanda ake zargi a kafafen yaɗa labaran gwamnati.
Kafar yada labaran Aljazeera ta ruwaito cewa cikin waɗanda aka kama har da Janar Abass Dembele, tsohon gwamnan yankin Mopti wanda aka sauke daga mukaminsa bayan ya bukaci a binciki zargin sojojin Mali sun kashe fararen hula da kuma Janar Nema Sagara, wadda ta yi fice wajen yaki da ’yan tawaye a shekarar 2012. Majiyoyin tsaro sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kama akalla sojoji 55, kuma bincike na ci gaba domin gano sauran masu hannu a lamarin. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ɗumamar dangantaka tsakanin Mali da Faransa, inda shugabannin soja ke zargin Paris da tsoma baki.
Mali na fama da matsalar tsaro tun daga shekarar 2012, sakamakon hare-haren ’yan bindiga masu alaƙa da ƙungiyoyin al-Qaeda da ISIS da kuma ’yan ta’addan cikin gida. Karkashin shugabancin Janar Assimi Goita, gwamnatin sojan ta janye daga hulɗa da ƙasashen yamma, tare da komawa ga Rasha wajen siyasa da tsaro. Duk da alƙawarin da ta yi na mika mulki ga farar hula a Maris 2024, a watan Yuni aka ƙara wa Goita karin shekaru biyar a kan mulki, lamarin da ya ƙara karfafa ikon sojoji a ƙasar.