Hukumar bada agajin gaggawa ta Kasa NEMA, tace har yanzu tanaci gaba da aikin ceton mutane bayan kifewar wani jirgin ruwa a jihar Sokoto da yayi sanadiyyar batan gwamman mutane.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bayyana cewa, jirgin wanda ke dauke da fasinjoji sama da 50 da ke a kan hanyarsu ta zuwa kasuwa ya kife ne da safiyar Lahadi.
Hukumar tace a halin yanzu Mutane 10 ne aka iya cetowa, yayin wasu da dama kuma sukai batan dabo da har yanzu ake ci gaba da nemansu.

Ana fargabar mutane 30 sun hadu da ajalinsu a lokacin da kwale-kwale ya kife da su cikin kogi a jihar Sokoto
-