Hukumar Shirya Ziyarar Ibadar Kiristoci ta Najeriya (NCPC) ta tabbatar da cewa za a ci gaba da aikin hajjin Kirista zuwa Isra’ila da Jordan a watan Satumba, bayan dakatar da shi da aka yi sakamakon rikicin da ya kunno kai a Gabas ta Tsakiya. Babban Sakataren Hukumar, Bishop Stephen Adegbite, ya bayyana hakan bayan dawowarsa daga Isra’ila, inda ya tabbatar da cewa yankin yanzu ya samu nutsuwa.
Jaridar Punch wacce ta ruwaito labarin ta ce Adegbite ya ce Gwamnatin Tarayya ta amince da rage kuɗin kujerar zuwa ibadar ta Kirista da kashi 50%, wanda hakan ke nufin cewa masu niyya za su biya rabin kuɗin kawai. Ya ƙara da cewa aikin zai ɗauki kwanaki goma, kuma za a kaddamar da shi ne a ranar 14 ga Satumba, 2025 daga jihar Imo.
Dangane da batun tsaro, shugaban NCPC ya bayyana cewa hukumar ta tanadi matakan kariya domin kauce wa duk wata barazana. Ya tuna yadda aka taba karkatar da jerin maniyyata na kasar zuwa Jordan lokacin wani rikici, inda ya ce, “duk wanda ya tafi tare da mu, zai dawo lafiya.”
Bishop Adegbite ya kuma ce kafin kaddamar da aikin, zai jagoranci wata tawaga ta mambobin Majalisar Wakilai kusan 100 zuwa Isra’ila. Ya jaddada cewa duk da kalubalen da aka fuskanta a baya, ibadar ta Kirista ta kasance al’ada mai kyau tun daga 1999, tare da tabbacin kariyar Allah da kuma tallafin gwamnati wajen tabbatar da nasarar wannan ziyara ta 2025.