Jam’iyya mai mulki wato APC ce ta fi rinjaye inda ta lashe kujeru 12, sai PDP da ta samu nasara a Ibadan din jihar Oyo yayin da NNPP tayi nasara a Kano, sannan APGA ta lashe mazabu biyu a Jihar Anambra.
Biyo bayan hakanne yasa jam’iyyar ADC bayyana rashin jin dadin ta da yadda aka gudanar da zaben, tana zargin cewa an yi amfani da barazana da cin hanci a lokacin gudanar da zabukan.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar ta ADC na kasa Bolaji Abdullahi ya fitar yace zaben cike ya ke da magudi ta hanyar sayan kuri’u da tashe-tashen hankula.
