DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hisbah a jihar Kano za ta dauki nauyin aurar da tubabbun ‘yan daba

-

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana shirin ta na ɗaukar nauyin auren wasu matasa da suka ajiye makamai tare da yin alkawarin barin ayyukan daba da tashin hankali.

Kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana haka bayan sama da matasa 1,000 sun ajiye makaman su tare da rungumar zaman lafiya.

Google search engine

Sheikh Daurawa ya ce wannan shiri na daga cikin manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wajen ba da damar gyara rayuwa da inganta makomar matasa da ke aikata laifi.

Ya gargade su da su zama mutane na gari tare da kira da sauran da ke irin wannan dabi’a su dawo domin rungumar zaman lafiya.

An gudanar da taron ne a Hedikwatar hukumar ‘yan sandan jihar Kano da ke Bompai,tare da sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara