Jami’an sashen binciken laifuka CID,a Sri Lanka sun kama tsohon shugaban ƙasar, Ranil Wickremesinghe, bisa zargin amfani da kuɗaɗen gwamnati ba bisa ka’ida ba.
Wickremesinghe, mai shekaru 76, ya bayyana a ofishin CID a Colombo domin bayar da bayani kan wani bincike da ya shafi tafiyarsa zuwa Landan a shekarar 2023, inda ya halarci bikin kammala karatun matarsa a Jami’ar Wolverhampton.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban ya je Landan ne daga Havana bayan taron ƙungiyar G77.
CID na zargin cewa an yi amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen tafiyar, ciki har da biyan kudin tsaro na jami’an da ke tare da shi.
Sai dai Wickremesinghe ya dage cewa matarsa ce ta biya kuɗin tafiyarta, kuma bai taɓa amfani da kuɗin gwamnati ba,hakan ya sa jami’an tsaro suka fara tambayar wasu daga cikin ma’aikatansa tun kafin wannan lokaci.