DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba za a tsawaita wa’adin biyan kudin hajji a bana ba – NAHCON 

-

Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta ce hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa ba za a ƙara wa’adin biyan kuɗi, ɗa kuma sauran shirye-shirye na aikin hajjin 2026 ba.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana hakan a taron da aka yi da kamfanonin da ke da lasisin gudanar da aikin hajji, inda ya jaddada muhimmancin bin jadawalin da Saudiyya ta gabatar.

Google search engine

Kwamishinan ayyuka na hukumar, Prince Anofiu Elegushi, ya gargadi masu kokarin zuwa da su guji jinkiri, inda ya ce a wannan lokacin idan aka rufe an rufe kenan babu karin lokaci.

Ya ce a bara wasu kamfanoni sun yi sakaci da tsammanin za a ƙara wa’adi, abin da ya sa suka rasa damar zuwa, lamarin da ya zama babban darasi domin hajjin bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara