Kocin kungiyar Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana dan wasan tsakiyar kulob din, Rodri, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2024, a matsayin dan wasa mafi kyawu a duniya na duk da samun raunuka da ya fuskanta a kakar da ta gabata.
Guardiola ya tabbatar da cewa Rodri ya dawo cikin koshin lafiya kuma zai iya bugawa a wasan City da Tottenham da za a yi ranar Asabar a gasar Premier League.
Rodri ya sha wahala a kakar bara bayan ya samu mummunan rauni a gwiwa a fafatawar da Man City ta yi da Arsenal a watan Satumba.
Wannan ya sa ya rasa buga wasanni da dama,sai dai matsalar ta sake kunno kai har ta hana shi buga wasa a farkon wannan kakar, ciki har da wasan da City ta doke Wolves da ci 4-0 makon da ya gabata.