DCL Hausa Radio
Kaitsaye

A duba zargin rashawa da ake yi wa jami’an gwamnatin Kano – Kungiyoyin farar hula

-

Kungiyoyin al’umma a ƙarƙashin League of Civil Society Organisations a jihar Kano sun bukaci gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ɗauki matakin gaggawa kan zargin rashawa da ake yi wa wasu manyan jami’an gwamnati.

Kungiyoyin sun bayyana cewa lamarin ya nuna mummunan tsarin cin hanci da wofantar da amana, wanda zai iya tasiri wajen korar masu sha’awar zuba jari a jihar.

Google search engine

Sun ce binciken ICPC da EFCC ya gano badakala guda biyu, ciki har da na shugaban hukumar zaɓe ta Kano (KANSIEC), Sani Malumfashi, tare da sakataren hukumar Anas Mustapha da wani mataimakin darakta a sashen kuɗi.

Rahoton ya nuna sama da N1bn aka karkatar daga asusun hukumar a Unity Bank, inda aka mayar da shi zuwa wani kamfani na kashin kai da sunan biyan ma’aikatan wucin gadi, duk da cewa an riga an biya su ta banki.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kungiyoyin sun yi gargadin cewa rashin ɗaukar mataki mai ƙarfi daga gwamnati kan iya lalata amincewar jama’a da kuma kawo cikas ga ci gaban Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara