Rundunar ‘Yan sandan jihar Nasarawa ta kama shahararren shugaban ‘yan garkuwa da mutane da fashi da makami, Mohammed Bammi wanda aka fi sani da Zomo, a karamar hukumar Doma.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Ramhan Nansel, ya ce an damke shi ne yayin aikin share dajin Doka, inda ya yi ƙoƙarin kai wa jami’ai hari da wuka kafin a rinjaye shi.
Bincike ya kai jami’an tsaro zuwa maboyar su a ƙauyen Alagye, inda aka kwato bindigogi, harsasai, kayan sawa na jami’an tsaro, da sauran abubuwa.
Haka kuma, a wani samame daban a ƙauyen Gidan Taku, Awe LGA, rundunar ta kama wasu mutum biyar daga cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane guda goma.
Jaridar Punch ta ambato kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Shetima Mohammed, na yaba wa da nasarar jami’an rundunar tare da jan kunne cewa za su ci gaba da ƙara tsananta wa ‘yan ta’adda har sai an tsarkake jihar.



