Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya ce makomar haɗin kan jam’iyyun adawa a zaben 2027 za ta dogara ne kan wanda za a zaɓa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.
Lamido ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Daily Trust, inda ya yi tsokaci kan rade-radin yiwuwar haɗa kai da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, makomar jam’iyyar PDP da kuma dalilin da ya sa yake ganin zaɓen ɗan takara da bai dace ba zai iya raunana ƙarfin haɗin kan jam’iyyun adawa.
Da aka tambaye shi game da rade-radin cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya zaɓe shi a matsayin mataimakin Jonathan a zaben 2027, Lamido ya ce labarin abin dariya ne.
Sai dai rahoton Daily Trust ya ruwaito shi yana gode wa al’ummar Najeriya da suke ganin daraja da cancantarsa, yana mai cewa ya yi mamaki da irin kallon da ake masa.



