Kamfanin sadarwa na MTN yabayyana cewa ya kammala aikin gyaran hanyar sadarwar da ya shafi rukunin sadarwa guda 101 a cikin kananan hukumomi 15 na jihohin Adamawa, Borno da Kano.
Kamfanin sadarwar ya fitar da sanarwa a ranar Litinin cewa maido da hanyoyin ya kasance babban mataki a ci gaban kokarinsa na inganta sahihancin ‘sabis’ a yankin Arewa maso Gabas, duk da yawan matsalolin yankan layin fiber da kuma barna.
Aikin gyaran, wanda aka gudanar a ranar Lahadi, 24 ga watan Agusta, ya haɗa da sauya hanyar zirga-zirgar sadarwa zuwa sabon layin fiber da aka girka a kan hanyar AFCOT–Bawo Village a Jihar Adamawa.