DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rahotanni da Hirarrakin DCL Hausa a Bikin Ranar Hausa ta Duniya 2025

-

 

Kowace shekara a ranar 26 ga watan Agusta, al’ummar Hausawa a sassa daban-daban na duniya na murnar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A bana, 2025, DCL Hausa ta gudanar da wannan rana ta musamman da jerin shirye-shirye daban-daban — daga sakonnin fitattun mutane, hira da masana, jin ra’ayoyin jama’a a kan titi, rera wakar baka har zuwa tattaunawa da jama’a ta kafafen sada zumunta.

Google search engine

Manufarmu ita ce nuna karfi, grima da tasirin harshen Hausa tare da gabatar da tattaunawa da za ta ilmantar da al’ummarmu. Ga takaitaccen jerin dukkan bidiyo da hotunan da muka wallafa domin tunawa da wannan rana ta tarihi.

Sakon Fitattun Mutane: Sakon Bulama Bukarti, Ali Nuhu da sauran fitattun jarumai kan Ranar Hausa ta Duniya

Karin Harshe da Wakoki: Shin tsakanin Hausar Kano da ta Sokoto wace ta fi dadi? Ga Fauziyya Jantullu mai baza capacity da Hausar Sokoto

Hausa a Kasashen Waje : Yadda na kwashe shekaru takwas ina koyar da Hausa da al’adun Hausawa ga Turawa a Jamus — Dr. Muhsin Ibrahim

Rahoton Bidiyo na Sharhi: Yadda Hausa ta zama harshen kabilu sama da 100 a Arewacin Nijeriya

Muna bukatar ECOWAS ta ayyana Hausa a matsayin harshen kasa a Nijeriya da Nijar – Jagoran Ranar Hausa, Abdulbaki Jari

Tattaunawa da Jama’a: Za ku iya karasa mana wadannan karin maganar na Hausa?

Gwada Basira: Ina ma’abota social media, ku zo ku fassara mana wadannan kalmomin albarkacin Ranar Hausa ta Duniya

Ra’ayin Masana: Daliban Hausa a makarantun gaba da sakandare na fama da kalubale masu yawa — Dr. Abdurrahman Aliyu

Hausa a Fina-finai : Yadda muka kirkiro kalmomin suburbuda da achawi, da jegare, saqago – Jagoran masu fassara fina-finan Indiya zuwa Hausa, Sadik Salihu Abubakar

Kammalawa 

Da wadannan shirye-shiryen, DCL Hausa ta yi bikin Ranar Hausa ta Duniya 2025 ta hanyar haskaka fadin harshen Hausa, tasirinsa da kuma rawar da yake takawa a duniya — ta bakin fitattun jarumai, masu fafutuka, mawakan baka da jama’an gari a tituna. Wannan rubutu kuma zai kasance tushen tunawa gare mu da masu kallonmu domin ganin yadda muka gudanar da bikin ranar Hausa a bana, tare da tabbatar da cewa DCL Hausa na ci gaba da bunkasa harshen Hausa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hadimin Gwamna Abba Gida-Gida ya maka Jaafar Jaafar a kotu kan zargin sa da badakalar 6.5B

Hadimin gwamnan Kano Abdullahi Rogo ya maka mawallafim Jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar a kotu bisa wallafa labarin zargin almundahanar naira biliyan 6.5 Rogo na son...

Yadda na rasa ɗiyata da jikokina sanadiyyar shan ‘Dettol’ a matsayin magani

Rashin sani ya haddasa mutuwar yata da jikokina bayan da suka sha Dettol a matsayin magani Wata dattijuwa mai suna Asiya Hassan da ke zaune a...

Mafi Shahara