Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya shawarci al’ummomi su kiyaye da kuma kula da ayyukan da gwamnati ke shimfiɗawa a yankunansu.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kaddamar da wasu ayyuka a karamar hukumar Ika ta jihar Akwa Ibom.
Jaridar Punch ta ruwaito Akpabio ya ce jama’a su ɗauki wadannan ayyuka a matsayin mallakinsu, domin idan aka lalata su, to an cutar da al’umma gaba ɗaya.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na da niyyar kawo sauƙi ga talakawa ta hanyar samar da tallafi da ingantattun ayyuka.