A wani yunkuri na bunkasa masana’antun cikin gida, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da dokar hana fitar da kwallon kadanya wanda ake sarrafawa wajen samar da Man kaɗai har na tsawon watanni shida.
Umurnin, wanda zai fara aiki nan take ya biyo bayan rahotannin tafka asara da Najeriya ke yi sakamakon ficewa da danyar kadanyar kafin sarrafawa, yin hakan a cewar gwamnatin zai dakile kasuwanci mara riba da karfafa masana’antun cikin gida.
Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima, wanda ya sanar da dakatarwar a yayin wani taron masu ruwa da tsaki, ya bayyana cewa matakin zai ƙara darajta kasuwancin man kaɗai ta hanyar farfado da masana’antun sarrafa kayan gida, ta yadda za su samar da ayyukan yi da ƙarin kudaden shiga ga mazauna karkara musamman mata.
Shettima ya yi hasashen cewa sake tsara kasuwancin kaɗanya zai taimaka wajen samar da ribar kusan dala miliyan 300 a duk shekara.
Duk da cewa Najeriya ce kan gaba wajen noman kadanya a duniya, a halin yanzu bata mallakin fiye da kashi 1% daga ribar dala biliyan 6.5 da Kwallon ke samarwa a kasuwannin duniya.
A cewar ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, an kiyasta cewa Najeriya na asarar kimanin tan dubu 90 na danyen man kadanya a duk shekara sakamakon rashin bin ƙa’idojin cinikayya na bai ɗaya.
Ana sa ran matakin da zai biyo bayan dakatarwar zai taka rawa waken rage dogaron da Najeriya ke yi da man fetur wajen samar da kudaden shiga
Tuni kasashe masu makwabtaka da Najeriya da suka hada da Ghana, Burkina Faso, Mali, da Togo suka dauki irin wannan mataki don farfado da kasuwancin ƙwallon ƙadanya a ƙasashensu.