DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Kebbi Nasiru Idris ya naɗa sabon Sarkin Zuru

-

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya amince da naɗin Sanusi Mika’ilu-Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru.

Mai magana da yawun gwamnan, Ahmed Idris, ya bayyana haka a wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi a ranar Alhamis.

Google search engine

Jaridar Daily Nigerian ta ambato kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautu ta jihar, Garba Umar-Dutsin-Mari, na sanar da naɗin, yayin da ya mika takardar tabbatarwa ga sabon sarki a Zuru.

Kwamishinan ya ce daga cikin ƴan takara uku da suka nemi kujerar, bayan kwamitin zaɓen masarautar ya tantance su, Sanusi Mika’ilu-Sami ne ya samu mafi yawan ƙuri’u da suka ba shi damar hawa gadon sarautar Zurun.

An naɗa shi ne sakamakon rasuwar tsohon Sarkin Zuru, Muhammad Sani-Sami Gomo II, wanda ya rasu a ranar 16 ga Agusta, 2025, a wani asibiti da ke Landan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

APC yaudarar ‘yan Nijeriya take a batun bude tikitin takarar shugaban – In ji CUPP

Ƙungiyar hadakar jam’iyyun hamayya a Nijeriya (CUPP) ta ayyana sanarwar da jam’iyyar APC mai mulki ta yi cewa tikitin shugabancin ƙasa na 2027 a buɗe...

Ina nan daram a NNPP, babu inda zan je – Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ba shi da...

Mafi Shahara