DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Yadda na rasa ɗiyata da jikokina sanadiyyar shan ‘Dettol’ a matsayin magani

-

Rashin sani ya haddasa mutuwar yata da jikokina bayan da suka sha Dettol a matsayin magani

Wata dattijuwa mai suna Asiya Hassan da ke zaune a garin Shinkafi na jihar Katsina, ta shaida ma DCL Hausa yadda wani lamari mai ban tausayi da darasi ya faru da diyarta da take aure a kauyen Abukur shi ma a jihar Katsina wanda ya yi sanadiyyar rasuwar yarta.

Google search engine

Asiya Hassan ta bayyana cewa ‘yarta na dauke da tsohon ciki ta kuma ziyarci asibiti domin duba lafiyarta da ɗan da take dauke da shi a cikinta.

Likita ya rubuta mata magunguna, ta je ta saya, daga ciki akwai maganin wanke bayi wato ‘Dettol’, sai ta hada da shi ta sha tare da sauran magungunan da ta saya.

“Ta sha marfin Detol biyu, kamar yadda ta sha sauran magungunan. A ganinta shi ma magani ne”.

“Tana da yaro shi ma ta ba shi marfi daya, bayan ya yi mata kuka cewa shi ma baya da lafiya, abin ka da yaro, ashe karar kwana ce” in ji Asiya

“Bayan kwana daya da faruwar lamarin sai nakuda ta zo mata, ta haifi yaronta tun kafin lokacin haihuwarsa ya yi, amma yaron ya koma ga mahaliccinsa, ita ma daga bisani ta ce ga garinku nan, yaron nata shi ma ya bi bayanta” a cewar dattijuwar.

Asiya Hassan ta shaida ma DCL Hausa cewa rashin ilimi ya taka muhimmiyar rawa wajen faruwar lamarin, saboda rashin halartar makaranta da diyarta ba ta yi ba kafin a aurar da ita da ma bayan an aurar da ita.

Daga karshe Asiya Hassan ta yi kira ga iyaye su saka yaransu makaranta domin rashin ilimi babban ciyo ne a rayuwa.

A yanzu dai Asiya Hassan na neman taimako ga masu hannu da shuni na ganin an dauki nauyin karatun sauran yaranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Zan zaɓi Tinubu muddin ‘yan Adawa suka tsayar da Peter Obi a 2027 – Adeyanju

Mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Deji Adeyanju, ya bayyana cewa zai ba da ƙuri’arsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 idan dai...

Ma’aikatan manyan kwalejojin fasaha sun ba gwamnatin Nijeriya sabon gargadi

Kungiyar ma'aikatan manyan kwalejojin fasaha a Najeriya (SSANIP) ta sake bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 domin ta magance duk matsalolin da suka dade...

Mafi Shahara