Ƙungiyar hadakar jam’iyyun hamayya a Nijeriya (CUPP) ta ayyana sanarwar da jam’iyyar APC mai mulki ta yi cewa tikitin shugabancin ƙasa na 2027 a buɗe yake ga dukkanin mambobinta duk da goyon bayan da ta bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin yaudara ga ‘yan Nijeriya.
Sakataren CUPP na Ƙasa, Peter Ameh, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sakataren tsare-tsare na ƙasa na jam’iyyar APC, Sulaiman Argungu, ya ce jam’iyyar ba za ta rufe ƙofa ga kowane ɗan takarar da ke sha’awar tsayawa takara ba, duk da goyon bayan tazarce da ta bai wa Tinubu.
Tuni goyon bayan da aka bai wa Shugaba Tinubu daga manyan jiga-jigan jam’iyyar ya nuna cewa an riga an da an ƙudurce sakamakon zaɓen fidda gwanin jam’iyyar.
Wani mataki da ke nuna rashin gaskiya da rashin adalci a tsarin APC, in ji sanarwar da kungiyar ta CUPP ta fitar.