Hadimin gwamnan Kano Abdullahi Rogo ya maka mawallafim Jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar a kotu bisa wallafa labarin zargin almundahanar naira biliyan 6.5
Rogo na son kotu ta kwato masa hakkinsa bisa zargin da yake wa Jaafar Jaafar da rubuta labarin da ya bata masa suna, da shi da mai gidansa gwamnan Kano.
Baya ga Jaafar Jaafar, hadimin na gwamnan Kano ya maka Audu Umar da ke aiki da mawallafin na Jaridar Daily Nigerian.
Tuni alkali Abdulazeez M. Habib na kotu ta 15 da ke Nomansland ya bukaci rundunar yansanda da ta kaddamar da bincike mai zurgi kan wannan zargi.
Hakan na zuwa ne yayin da hukumomin EFCC da ICPC masu yaki da cin hanci a matakin tarayyar ke ci gaba da bincikar hadimin, daidai lokacin da Daily Nigerian ta ruwaito cewa tuni Abdullahi Rogo ya dawo da naira biliyan 1.1 cikin kudaden da ake zargin ya yi badakalarsu.