Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ba shi da niyyar barin jam’iyyarsa duk da jita-jitar siyasar da ake yadawa a shirye-shiryen zaɓen 2027.
Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a birnin Abuja yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na tara na jam’iyyar, inda ya tabbatar wa shugabanni da magoya baya cewa babu wani shirin da ya shafi ficewarsa daga NNPP.
Jaridar The Nation ta ambato Kwankwaso ya ce suna da tabbacin cewa suna da abin da za su bayar a ƙarshe wajen shugabancin ƙasar nan, amma suna so su yi shi yadda ya kamata.