Kungiyar ma’aikatan manyan kwalejojin fasaha a Najeriya (SSANIP) ta sake bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 domin ta magance duk matsalolin da suka dade suna jawo ce-ce-ku-ce tsakanin bangarorin, ko kuma ta fuskanci yajin aiki a fadin ƙasa.
Wa’adin, wanda ya fara aiki tun daga ranar 27 ga Agusta, 2025, na ƙunshe ne a cikin sanarwar ƙarshe da aka fitar a taronta karo na 77 na majalissar koli ƙungiyar, wanda aka gudanar a Kwalejin Noma ta Audu Bako, Danbatta, Jihar Kano.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa, a cikin sanarwar, ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda gwamnati ke nuna rashin gaskiya wajen warware matsalolin da suka jima suna jiran mafita.