Mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Deji Adeyanju, ya bayyana cewa zai ba da ƙuri’arsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 idan dai haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC ta tsayar da Tsohon ɗan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, a matsayin wanda zai nemi shugabancin ƙasa.
Adeyanju ya yi wannan magana ne a ranar Juma’a a cikin shirin Morning Brief na gidan talabijin na Channels, lokacin da aka tambaya shi ko manufarsa ita ce ɓata sunan Obi.
Akwai dadaddiyar tsamin alaka tsakanin Obi da lauya Adeyanju tun bayan da ya zargi Obi da ƙarfafa muguwar al’adar siyasa ta “Obidients” wato makafi a siyasance.