Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Enduring Peace domin magance matsalar tsaro da ta addabi jihar Filato da wasu sassan Bauchi da Kaduna.
An ƙaddamar da rundunar ne a hedikwatar rundunar sojojin Najeriya ta 3 Division da ke Rukuba Barrack, Jos, domin ta maye gurbin tsohuwar rundunar Operation Safe Haven.
Yayin taron ƙaddamarwar, babban hafsan sojin ya bayyana cewa sabuwar rundunar wani sabon fasali ne aka yi wa Safe Haven, domin tabbatar da dawwamammen zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa tare da sulhunta al’ummomi.
Janar Musa ya jaddada cewa Operation Safe Haven ta taka rawar gani wajen rage matsalolin tsaro a yankin, inda ta ba da tabbacin tsaro ga al’ummomin da suka dade suna fama da tashin hankali.
Ya ce sabon salo na Operation Enduring Peace zai ɗauki matsayi mafi faɗi, tare da sabuwar manufa da ƙuduri na tabbatar da tsaro da zaman lafiya mai ɗorewa, ba kawai na ɗan lokaci ba.
Babban hafsan sojin ya kuma jaddada bukatar haɗin kai tsakanin sojoji da al’umma, yana mai cewa amincewa daga jama’a ba a saya ake yi ba, sai ta hanyar aikata abin da ya dace.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su mara wa rundunar tsaro baya domin tabbatar da zaman lafiya da kiyaye doka da oda a dukkan faɗin ƙasa.