Solomon Arase mai shekara 69 ya rasu ne a ranar Lahadi a asibitin Cedar Crest da ke Abuja, babban birnin tarayya.
Wani ɗan uwansa ya tabbatar da rasuwar a hirar wayar da suka yi da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na ƙasa, Muyiwa Adejobi, shima ya tabbatar da hakan, inda ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwa daga hukumomin ƴan sanda.
Arase, wanda ya kasance Sufeto na 18 a tarihin ƴan sandan Najeriya, daga bisani an naɗa shi Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ƴan sanda (PSC).
