DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan jihar Neja Umar Bago, ya sauke dukkanin kwamishinoninsa

-

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sauke dukkanin kwamishinoninsa, tare da umartar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar da su ci gaba da rike ragamar ma’aikatun har zuwa lokacin da za a nada sababbin kwamishinoni.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a Litinin din nan yayin taron majalisar zartarwa, inda ya yi gargaɗi ga tsoffin kwamishinonin da kada su yi yunƙurin neman taimako ko shiga sahun masu neman mukaman gwamnati.

Google search engine

Ya ce cikin mako guda zuwa biyu zai sanar da sabuwar majalisar zartarwa, inda ya bayyana cewa ya riga ya yi nazari kan ayyukan kowanne daga cikin tsoffin kwamishinonin.

A cewarsa, akwai wadanda suka taka rawar gani a ayyukansu, yayin da wasu kuma ba su samu damar yin ayyukan da aka dorasu akai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara