Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS) ta sanar da cewa za ta karrama fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, wanda za a ba shi digirin girmamawa na Doctor of Letters (D.Litt), Honoris Causa.
Wannan karramawa na zuwa ne bisa jajircewarsa wajen ilimi, gyaran zamantakewa, da kuma kokarinsa na yada zaman lafiya a Najeriya da ma kasashen waje.
Shugaban Jami’ar Farfesa Bashir Garba ne ya bayyana hakan, a yayin taron manema labarai gabanin bikin cikar jami’ar shekaru 50 da kuma yaye daliban da suka kammala karatu karo na 42.
Haka kuma, tsohon Shugaban Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Faruku Yahaya (Rtd.), zai samu lambar girmamawa ta Doctor of Science (D.Sc.), Honoris Causa, bisa gudummawarsa ga harkokin tsaro da kare martabar kasa.
Jami’ar ta bayyana cewa wannan karramawa wani yunkuri ne na girmama mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wajen raya kasa, ilimi da zaman lafiya.
Bikin zai kasance babban abin tarihi yayin da dubban dalibai za su karɓi takardunsu, tare da nuna irin gudummawar UDUS ga ci gaban ilimi da zaman lafiya a Najeriya tun daga 1975 zuwa yau.



Wannan karramawa da Jami’ar UDUS za tayi wa Sheikh Daurawa gaskiya abin a yaba ne duma da irin Gudunmawar da yake bayarwa ta ko wane Bangare. Ubangiji Allah ya qaro mana Ilimi mai amfani