DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Makircin siyasa ba zai hana Tinubu sake lashe zabe ba – Musa Iliyasu Kwankwaso

-

Jigo a jam’iyyar APC, kuma Daraktan kudi a ma’aikatar Hadejia Jama’are Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce duk wani kazafi ko Makircin irin na siyasa ba zai hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu sake lashe zabe a karo na biyu ba.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a martaninsa kan harin da aka kai wa tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami, da kuma taron shugabannin jam’iyyar ADC a Kaduna, inda ya ce duk wannan manakisar siyasa ce don bata sunan Shugaba Tinubu.

Google search engine

Ya ce, an taba yin shugabanni daga Arewa da dama kafin Tinubu, Buhari ma ya yi shekaru takwas amma yanzu ana kokarin bata sunan Tinubu.

A cewar sa, tsaro ya inganta matuka a karkashin mulkin Tinubu, domin kuwa ana bin hanyar Kaduna-Abuja lafiya, yayin da ‘yan bindiga ke tserewa a yankin arewa maso yamma.

Kwankwaso ya jaddada cewa, a yau akwai ayyukan ci gaban gine-gine da dama a Arewa, kuma Shugaba Tinubu ya bai wa ’yan Arewa manyan mukamai, ciki har da NSA, Mallam Nuhu Ribadu da CDS, Janar Christopher Musa.

Ya ce, wannan ne zai tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa Tinubu ya cancanci sake samun goyon baya a zaben 2027.

1 COMMENT

  1. Insha’allahu kuwa TINUBU sai ya fadi Zabe a 2027, don mu Talakawa mune ya kamata mu fadi wanda muke da Ra’ayin Zaba a 2027 ba wani qato ba. Don Wallahi bamu ga wani Qaton Matsiyaci ba da ya isa yazo yace wai zai Tallata mana TINUBU ba kuma wai har mu sake Zabar sa. Iliyasu Kwankwaso kake ko? To maganar gaskiya kana Yaudarar kanka ne kawai, wannan ita ce maganar gaskiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara