DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Zan ci gaba da yi wa ’yan Nijeriya hidima ba tare da nuna banbanci ba – Tinubu

-

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatin sa ba za ta nuna bambanci ba, wajen samar da ababen more rayuwa da ayyukan ci gaba ga yan kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya jaddada cewa rantsuwar da ya dauka ita ce yi wa dukkan ’yan kasa hidima ba tare da nuna bambancin siyasa ko yanki ba.

Google search engine

Ya lissafa manyan ayyuka kamar titin Lagos–Calabar, Sokoto–Badagry Superhighway, layin dogon Port Harcourt–Maiduguri, da hanyar Abuja–Kaduna–Kano a matsayin shaida cewa babu wani yanki da ake watsi da shi.

Shugaban ya kuma bayyana cewa gwamnati na samar da ayyukan yi ga sama da mutane 250,000, gyaran cibiyoyin lafiya a fadin Nijeriya, tare da dawo da wutar lantarki a Kaduna ta hanyar sabunta injinan samar da wuta mai karfin megawatts 255.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara