Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya soki yadda yan majalisun tarayyar kasar ke gudanar da ayyukan su, yana mai cewa sun fi wadanda suka gabace su muni.
Cikin wani sabon littafi da ya wallafa mai taken “Tarihin Najeriya da gobenta”, Obasanjo ya bayyana ayyukan mazabun majalisu a dukkanin matakai a matsayin fashi da rana tsaka.
Ya kara da cewa yadda suke gabatar da ayyuka ya nuna irin yunwar tara kudade ta haramtacciyar hanya da yan majalisun ke fama da ita, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya kara da cewa bai ga wata alamar kawo wa Najeriya ci gaba daga gare su ba, kamar yadda aka dabbaka a cikin kundin tsarin mulkin kasar.



