Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kara adadin kasafin kudin da take warewa bangaren lafiya da kaso 20.
Babban daraktan WHO a Najeriya Farfesa Mohammed Janabi ne yayi wannan kira a birnin Abuja, yayin taron tattaunawa kan harkokin kudade a fannin lafiya a Najeriya.
A cewar Janabi, samar da wadatattun kudade a bangaren lafiya zai tabbatar da dorewar ci gaban ‘yan kasa a fannin.



