“Yawancin ‘yan siyasar Nijeriya ba su da amana”, Jonathan ya fadi yadda ya ce an ci amanarsa a 2015.
Tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, ya ce ya fuskanci cin amana da dama a lokacin da yake neman sake zaben shugabancin kasar a shekarar 2015.
Jonathan ya bayyana hakan ne a wajen bikin cika shekara 70 na Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe da aka gudanar a Benin, babban birnin jihar Edo.
Ya ce, yawancin ‘yan siyasar Nijeriya ba su da amana.



