Wata kotu a Ghana ta yanke wa wasu ’yan Nijeriya uku hukuncin zaman kurkuku na shekaru 96 kowannen su bisa laifin satar motoci a birnin Kumasi.
An kama mutanen ne a ranar 20 ga Yuni, 2025, bayan an zargesu da satar motocin da aka yi a cikin birnin.
Hukuncin na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan karuwar aikata laifuka da ake zargin baki suna yi a ƙasar.
A watan Yuli dai, hukumar shige da fice ta Ghana ta kama ’yan Nijeriya 50 a Accra bisa zargin damfara ta yanar gizo da kuma fataucin mutane zuwa kasashen waje.



