Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta sanar da soke harajin kaso 5% da aka kakaba a kan harkokin sadarwa, ciki har da kiran waya da na data.
Hukumar sadarwar Nijeriya ta NCC ce ta tabbatar da hakan ta bakin shugabanta, Dr. Aminu Maida, inda yace shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bayar da umarnin cire wannan haraji a tattaunawa kan sabon tsarin haraji da aka amince da shi kwanan nan.
Dr. Maida ya bayyana cewa matakin zai rage zurarewar kuÉ—i da a’umma ke bayyana cewa suna fuskanta, tare da tallafa wa ci gaban tattalin arziki a zamance.




Hakan yayi dai Dai