Hukumar yaki da ayyukan rashawa a Nijeriya ta ICPC ta bayyana cewa ta bibiyi ayyuka 1,440 da darajarsu ta haura Naira biliyan 271 cikin shekaru biyu da suka gabata.
Shugaban hukumar, Dr. Musa Aliyu ne ya bayyana hakan yayin taron kwana guda da aka shirya tare da ‘yan jarida daga Arewa maso yamma da Arewa maso Gabas wanda ya gudana a jihar Kano.
Dr. Musa ya ce daga cikin ayyukan da aka bibiya a Arewa maso Gabas, an gano ayyuka 767 da darajarsu ta kai Naira biliyan 112 da miliyan 737.
Kazalika Arewa maso yamma, kuwa an gano ayyuka 673 da darajarsu ta kai Naira biliyan 158 da miliyan 317.
Ya ce babban abin lura shi ne yadda rahoton jaridu kan ayyukan da aka yi watsi da su ya taimaka wajen tabbatar da cewa an bibiyi wadannan aiyuka, domin ganin an aiwatar da su.
Shugaban hukumar ya ce an samu nasarar kwato kuɗi Naira biliyan 7 da miliyan 269, sai kuma sama da dala miliyan a Arewa maso yamma.
An kuma kwato miliyan 43 da dubu 335 a Arewa maso Gabas.



