Hukumar zaɓe ta Nijeriya INEC ta bayyana cewa ƙungiyoyi 14 ne kawai daga cikin ƙungiyoyi 171 da suka nemi rajista suka cika sharuddan farko na zama jam’iyyun siyasa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sam Olumekun, kwamishinan hukumar na ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Bayanai da wayar da masu zaɓe ya fitar a yau, Alhamis 11 ga Satumba, 2025.
INEC ta ce an tantance buƙatun ne bisa tanade-tanaden Sashe na 222 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa gyara), da Sashe na 79 na Dokar Zaɓe ta 2022, tare da Ka’idojin INEC na 2022.
Hukumar ta bayyana cewa ta wallafa sunayen ƙungiyoyi 14 da suka tsallake wannan mataki a shafinta na yanar gizo da sauran dandamalin ta na hukuma domin jama’a su gani.
INEC ta kuma jaddada cewa rajistar jam’iyyun siyasa aiki ne da zai ci gaba a ƙarƙashin doka, kuma tana bude ƙofa ga kowacce ƙungiya da ta cika sharuddan doka.



