DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta hana INEC amincewa da shugabancin su David Mark a jam’iyyar ADC

-

Kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarni na wucin gadi da ya hana hukumar zaɓen Nijeriya INEC amincewa da tsohon shugaban majalisar Dattawa, David Mark, da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin shugaban rikon kwarya da sakataren jam’iyyar hadaka ta ADC.

Umarnin wanda mai shari’a Emeka Nwite ya bayar, ya biyo bayan buƙatar da wani ɗan jam’iyyar mai suna Nafi’u Gombe ya shigar a ranar 2 ga Satumban 2025, kamar yadda channels TV ya wallafa.

Google search engine

A cikin karar, an saka jam’iyyar ADC a matsayin wadda ake ƙara ta farko, David Mark na biyu, yayin da Aregbesola shi ne na uku, INEC da tsohon shugaban jam’iyyar, Ralph Nwosu, suma an saka su a matsayin na huɗu da na biyar.

Kotun ta kuma hana INEC amincewa da David Mark da Aregbesola har sai an saurari karar da aka shigar a kan lamarin.

A baya, INEC ta wallafa sunayen David Mark da Aregbesola a shafinta na yanar gizo a matsayin shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar ADC, tare da wasu jami’ai kamar tsohon gwamnan Edo, Oserheimen Osunbor, Ibrahim Mani, da Akibu Dalhatu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara