Shugaban Jami’ar tarayya ta David Umahi, Uburu (DUFUHS), dake jihar Ebonyi, Farfesa Jesse Uneke, ya bayyana cewa akalla ‘yan Najeriya miliyan 24 ne ke fama da matsalar rashin gani.
Rahoton jaridar Punch ya ruwaito farfesan ya bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawa da manema labarai kan ayyukan Cibiyar Idanu ta zamani da kuma Institute for Eye Health, Visual Sciences Research na jami’ar, a Uburu, karamar hukumar Ohaozara, jihar Ebonyi.
Ya ce, binciken da aka gudanar ta Nigeria National Blindness and Visual Impairment Survey ya nuna cewa sama da kashi 4.2% na ‘yan Najeriya masu shekaru 40 da haihuwa sama sun makance.
Haka kuma, kimanin mutane miliyan 4.25 da ke da shekaru 40 zuwa sama suna fama da matsakaiciyar nakasa ko tsananin matsalar gani.
Ya jaddada bukatar mutane su rika yin gwajin ido akai-akai, wayar da kai ga al’umma, tare da samar da magani mai saukin samu da kuma farashi mai rahusa.



