Bayan ya rataye takalman sa a ƙarshen kakar wasa ta bara, tsohon ɗan wasan Barcelona da Liverpool, Thiago, ya koma Barcelona a cikin tawagar masu horarwa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Thiago Alcântara zai kasance cikin mataimakan Hansi Flick, wanda ya fara jagorantar Barcelona a wannan kakar.
An bayyana cewa Flick yana ganin Thiago a matsayin wanda zai ba da gagarumar gudun mawa ga sabuwar tawagar sa, inda zai taimaka wa ‘yan wasan tare da koyon ƙarin dabaru a matakin horarwa.



