Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin Amurka a ƙarƙashin shugabancin Donald Trump ta fara mayar da wasu ‘yan Nijeriya gida, a wani sabon shiri da ya kaddamar.
Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai a Accra.
Ya ce mutum 14 ne aka maido daga Amurka, ciki har da ‘yan Nijeriya da wani ɗan Gambia, an sauke su a Ghana, inda daga nan aka tura su ƙasashensu.
Mahama ya ce Ghana ta amince da karɓar ‘yan Afirka ta Yamma da Amurka ke maido wa, kasancewar ba sa buƙatar visa don shiga ƙasar, sai dai ya nuna cewa dangantaka tsakanin Ghana da Amurka ta fara yin sanyi saboda karin haraji da Amurka ta kakaba kan kayayyakin Ghana da kuma takunkumin visa ga ‘yan ƙasar.
A cewar rahoton, Nijeriya ta sha yin watsi da tsarin karɓar ‘yan kasar daga Amurka, tana mai cewa ba za ta lamunci matsin lamba ba.
A baya-bayan nan ma, Amurka ta mayar da wasu mutane zuwa ƙasashe irin su Eswatini, Sudan ta Kudu da Rwanda, abin da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ke kallo a matsayin take haƙƙin waɗanda aka tsare.



