DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Masu aikata laifi a Nijeriya sun yi mana fintinkau – Kayode Egbetokun

-

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke addabar ƙasar sun fi jami’an tsaro shiri ta fuskar kayan aiki, kuɗi da kuma dabaru.

Egbetokun ya bayyana haka ne a babban ofishin ‘yan sanda na ƙasa da ke Abuja, lokacin da ya gana da kwamandojin sashen kula da iyakokin ƙasar, yace ‘yan ta’addan da ake fuskanta a yau ba irin ƙananan kungiyoyin da ake gani a baya ba ne.

Google search engine

A cewarsa, suna da kuɗi, suna da makamai masu ƙarfi, kuma suna amfani da sabbin fasahohi, takardun bogi da hanyoyin sadarwa na zamani a boye.

Sufeton ya jaddada cewa jami’an tsaro ba za su iya yaƙar irin wadannan mutanen da tsoffin kayan aiki ba.

Ya jaddada cewa jami’an tsaro na buƙatar kayan aiki na zamani domin su iya tunkarar waɗannan ƙungiyoyi masu tsari da haɗin gwiwa daga wasu ƙasashen ketare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara