DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijeriya ta ce ba ta samu wata sanarwa a hukumance ba kan mayar da yan kasar Ghana daga Amurka

-

Gwamnatin Nijeriya ta ce ba ta samu wata sanarwa a hukumance ba dangane da maido da ‘yan kasar daga Amurka zuwa Ghana.

Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun tabbatar da cewa kasar Ghana ta karɓi wasu ‘yan Nijeriya tare da sauran ‘yan Afirka ta yamma da Amurka ta kora a karkashin sabon tsarin kasar.

Google search engine

Rahoton ya bayyana cewa shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, ya tabbatar da zuwan rukunin na farko na mutane 14 da aka koro, ciki har da ‘yan Nijeriya da wani dan Gambia.

Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta bakin mai magana da yawunta Kimiebi Ebienfa ta ce har yanzu ba ta samu wata sanarwa ta hukumance ba daga Ghana, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

Gwamnatin Nijeriya dai ta sha nuna rashin amincewa da irin wannan tsarin da Amurka ke yi na tura mutane zuwa kasashen da ba nasu na asali ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara