Ana hasashen ambaliyar ruwa a Gwarzo da Karaye jihar Kano, Jibia jihar Katsina da karin wasu sassan jihohin Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta yi gargadi cewa jihohi 11 na kasar na iya fuskantar mamakon ruwan sama da ka iya haifar da ambaliya daga Lahadin nan zuwa Alhamis.
Daga cikin jihohin da ake kyautata zaton haka akwai yankunan Gwarzo da Karaye a jihar Kano, sai Jibia a jihar da jihohin Adamawa, Benue, Nasarawa, Taraba, Delta, Neja, Kebbi da Zamfara.



