DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sanda na da saukin kai ga ‘yan Najeriya a yanzu – AIG Ajani Omolabi

-

Mataimakin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya shiyya ta 17 wanda ya hada da jihohin Ondo da Ekiti Mr. Ajani Omolabi, ya ce a halin yanzu jami’ai na da kyakkyawar alaka tare da saukin kai ga’ yan Najeriya.

Yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a Akure, Omolabi ya ce wannan ya biyo bayan tsarin gabatar da aikin dan sanda a zamanance, wanda ya ce yana taimakawa matuka wajen yaki da ayyukan laifi musamman a shiyyar.

Google search engine

Ya ce tsarin na bai wa jami’ai damar samun bayanai daga al’umma, tare da samun cikakkiyar fahimtar juna, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

Kazalika ya ce an bayar da jerin lakcoci da tarukan kara wa juna sani domin inganta ayyukan jami’an ‘yan sanda a fadin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara